Fasahar Sadarwa ta Zamani (C.I.T)

Da sunan Allah Mai yawan rahama,Mai jin kai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Masoyinmu Abin koyinmu Annabinmu Muhammadu dan Abdullahi. Bayan haka,Godiya da Yabo sun tabbata ga Allah wanda ya halicci dan adam ya kuma hore masa ilimi da hanyoyin isar da sako. Dukkan mai rayuwa a wannan zamani yana gani ko yana jin labarin irin ci gaban da ake samu a bangaren isar da sako daga wuri zuwa wuri cikin sauki. Tunda aka halicci duniya babu wani lokaci da mutanen duniya suka kasance kusa da junansu kamar wannan zamanin. A yanzu nisa baya zama hujjar rashin isar sako, a duk inda mutum yake a cikin duniya yana iya yin kururuwa a ji shi cikin da kankanen lokaci. Dukkan mai son yada wani labari yana iya yada shi ga sama da mutum dubu a cikin rabin rabin dakika (second). Wannan wata hikima ce da baiwa wadda Allah (S.W.T) ya hore mana mu mutanen wannan zamani. Sai dai abin tambaya, shine wai shin muna amfani da wannan falala ta hanyar daya dace ??? Duk wanda Allah Yasa ya karanta wannan to ya yiwa kansa hisabi.

Comments

Popular Posts