Kadan daga cikin Littafin AURE BAUTAR UBANGIJI


MA’ANAR AURE DA  MATSAYINSA  A MUSULUNCI

Aure a musulunci yana nufin xaura yarjejiniyar zaman tare  tsakanin namiji da mace, bisa qa’idojin da addinin musulinci ya shimfixa. Tun da mun ga cewa daga cikin ma’anar aure akwai umarni kan bin wasu  qa’idoji da addinin musulunci ya shimfixa, to ya zama dole  mu gane cewa ashe Aure ibada ne. Don haka idan kabi qa’idojin da Allah ya shimfixa wajen tafiyar da aurenka, hatta wajen saduwa da matarka, to babu shakka Allah zai ba ka lada, kamar yadda ya zo a cikin hadisi mai daraja. Haka kuma in kaqi bin qa’idojin da Allah Ya shimfixa, to akwai zunubi a kanka ko a kanki. Dalili kuwa shi ne, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faxa wa sahabbai cewa “Hatta saduwa tsakanin miji da mata akwai lada”. Sai sahabbai suka tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa “Shin akwai lada ma ga mutumin da ya sadu da matarsa alhali daxi ya ji?” Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya amsa da cewa “Da zai sanya shi (azzakarinsa) a inda Allah bai halatta masa ba, da ya samu zunubi

Comments

Popular Posts