Thursday, 17 July 2014

Zamani ! Zamani !! Zamani !!!

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai, godiya da yabo da kirari da jinjina su kara tabbata ga Shugaban Halittu, cikamakin Annabawa, shugaban Manzanni. Annabinmu, Masoyinmu, Abin koyinmu, Annabi Muhammadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da iyalan gidanSa da abokanSa da wanda suka bi hanyarSu har zuwa karshen al'amari.
Tabbas duk mai hankali da lura ya san muna cikin wani zamani mai cike da hayaniya da bankaura, zamanin da karya ta koma gaskiya, gaskiya ta koma karya, zamanin da mutunci ya koma kudi, kudi suka koma sune komai. Zamanin da iyaye suka koma 'ya'ya, Ya'ya suka koma iyaye, zamanin da baiwa ta koma Uwargiya, Uwargijiya ta koma baiwa, zamanin da baya ta koma gaba, gaba ta koma baya. Zamanin ci gaban mai ginin rijiya yana kara shiga kasa yana ganin yaci gaba, zamanin da ake girmama mara girma a kaskantar da mai girma. Zamanin da idan ka ce Allah sai a kalle ka a matsayin dan-kauye, Zamanin tafiya babu waiwaye, zamanin gudu babu jira, zamanin kowa ya tsira da kansa. Zamanin gaggawa, zamanin sauri ba wajen zuwa, zamanin bushewar zukata, zamanin kekashewar idaniya, zamanin yawan magana, zamanin karancin aiki, zamanin fada ba cikawa.
Ya Allah muna rokonKa da sunayenKa masu tsarki, don kadaitakar Zatinka Ya Allah, yadda ka sako mu ZAMANIN, Ya Allah Ka kare mu, Ka kare imaninmu.

Friday, 18 April 2014

Huda Academy

As salaamu 'alaykum

Huda TV has now launched Huda Academy. Huda Academy is an Islamic Studies website where you will find FREE courses as well as certificate courses all recorded in high quality format. Ma sha Allah, I don't think it is anything like it on the internet. You be the judge...

Here is the link for <a href="http://www.hudaonlineacademy.com">Arabic Studies</a> offered at Huda Academy...

Sunday, 23 February 2014

DUK WANDA YA GODEWA ALLAH, ALLAH ZAI KARA MASA !

Malamina kuma Da-uwana a Musulunci, Malam Aliyu Gamawa ya yi  rubutu a kan  wannan maudu'i mai matuqar muhimmanci, na karanta kuma naga dacewar in adana wannan rubutu a nan domin kai na da kuma sauran 'yan-uwa musulmi. Ga rubutun kamar haka;
Allah mai yawan kyauta ga bayin sa. Mu sani hakika samu da rashi duk na karkashin abinda Allah ya qaddara ga bawan sa. Kowa in ya dubi halin da yake ciki a rayuwa to tabbas zaiga yafi wani samun ni'ima da baiwa cikin rabon da Allah ya bashi na yadda yake gudanar da rayuwar sa. Hakanan shima wani ya fishi sannan yana daidai da wani.
Ma gane cewa fahimtar cewa kafi wani, kuma kaima wani ya fika sai mai natsuwa da hankali, don hakan yana da wuya ga kowa don jinya ta kwadayi da buri da dan adam ke da shi. Kuma ba abinda ke jawo gasa da juna cikin tara abin duniya da son mamaye komi sai rashin godewa Allah. Duk fa wanda ke godewa rabon da Allah ya bashi to ya dace wajen kama hanyar zama mumini mai yawan godiya.
Jama'a kowa yayi nazari sosai, ya kalli tsarin gudanar da rayuwa gaba daya, zaka samu rabon dukiya, ilimi, mulki, da samun duk abinda rai ke so daga Allah ne shi kadai. Kuma daidai gwargwado an bawa kowa rabon sa. Amma ita zuciya na cike da hankoron neman kari, ga jiki da son hutu, rai dangin goro.... Hutawar zuciya da hanyar samun sauki da rayuwa mai dadi itace kowa ya godewa Allah bisa rabon da aka bashi.
Halin mutum sai Allah.. Mu kalli dabi'ar rashin godewa Allah bisa rabon da aka bamu tabbas shike jawo mana tunani iri iri, da rashin hutawar zuciya, shine sanadin hassada, kuma yana jawo mana mugun nufi, wassu ya kaisu ga sabawa Allah ta hanyoyin sata, cin rashawa, kudin riba, algus, kisan kai, da sauran irin su. Haka nan rashin godewa Allah na bata tsakanin iyaye da 'ya 'yan su, yana wargaza zaman aure, munana zato ga makusanta, haddasa fitina cikin al'umma, da sauran irin su. Hakanan rashin godiya na kashe zuciya, da fadawa tarkon shaidan na yawan son kayan wani.
'Yan uwa na maza da mata, Allah mai rahma ne da kyauta mai yawa ga bayinsa a duniya da lahira. Kuma kowa baya wuce rabon sa. Sannan a sama ko kasa ba mai iya tareka daga samun abinda Allah ya hukunta zaka samu. Kuma duk mai yawan godewa Allah to tabbas Allah zai kara masa. Duk gabar rayuwa da ka samu kanka da zangon daka kai rabon ka ne daga Allah ana fatan ka gode sai a kara maka.
Tir da wanda ya samu yayi alfahari, da wanda ya bar Allah ya koma ga masihirta da bokaye, ko mai dauka zurfin tunaninsa, da tulin hikima da wayonsa ne jagorar samun wani abu a gareshi. Da mai buga kirji yana kirari da yawan ilimi ko dukiyar sa. Ko mai yawan gori da raina mutane. Muna rokon Allah ya shirye mu.
Madallah da rayuwar bayin Allah masu tsentseni, da masu natsuwa da saukin kai cikin dukkan mu'amala. Masu godewa ni'imar da Allah ya basu. Da masu murna da yabawa dan rabon da Allah ya basu

Tuesday, 28 January 2014

Begen Annabi


  1. Allahu Shi bani sani da basira, In yi yabo bakin karfina
  2. In yabi Sidi Muhammadu Bawa, Mai hana sauran bayi kuna
  3. Yi dadin tsira Allah da aminci, Gun Manzonka dare har rana
  4. Da alolinsa da kau kau sahabbansa, Masu sanin darajojin juna
  5. Da matayensa, da 'ya'yayeansa, Da mu mabiyansa darea har rana