ZINA !!!

Lafazin Zina a shari'ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure ba ko an mallake ta. Haka nan akan yi amfani da lafazin zina akan abin da ba kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a hadisi Abi Huraira (R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "An rubuta wa xan Adam rabonsa na zina babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damqa, zinar qafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwaxayi tana fata, farji kuma shi yake gaskata haka ko ya qaryata" Muslim.
          A cikin wannan hadisi zamu ga yadda Manzon Allah (S.A.W) ya nuna cewa kowane xan Adam an rubuta masa rabonsa na zina, kuma zai sami wannan rabo babu makawa, sai dai ba za a kama shi da laifi ba har sai idan ya gasgata abin da idonsa ko kunnensa ko hannunsa ko qafarsa suka jiyar da shi, ta hanyar yin amfani da farjinsa don biyan buqatar waxannan gavvai, wannan shi ne ma'anar faxin Manzon Allah a qarshen hadisin da ya ce, "farji shi yake gasgata haka ko ya qarya ta" (Duba Sharhi Sahih Muslim Na Imam Nawawi J 16 sh 216).
            Sannan wannan hadisi yana nuna mana cewa ana amfanin da lafazin zina akan abin da bai kai ga saduwa ba, amma duk da haka ba a bashi hukuncin zina na jifa ko bulala. 
Hukuncin Zina A Musulunci
       
Zina haramun ce a addinin musulunci, Allah maxaukakin Sarki ya haramta ta in da yake cewa "Ka da ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma tafarki ne mummuna" (Isra'i : 32). Malamai suna cewa faxin Allah ka da ku kusanci zina, ya kai matuqa wajen hana ta, don ya fi a ce "kada ku yi zina".
          Sheikh Abdur-Rahman Assa'idiy yana cewa : "Hani ga a kusanci zina ya fi kai matuqa akan hana yin ta, saboda cewa kada a kusance ta ya haxa hana dukkan yin abubuwan da suke gabatarta kuma suke kawo yin ta, domin kuwa duk wanda ya yi kiwo a gefen shinge to ko yana daf da faxawa cikinsa, musamman ma akan irin wannan lamari, wanda da yawa daga cikin zukata suna xauke da abin da yake sa wa a afka masa. Sannan Allah ya siffata zina da cewa alfasha ce, ma'ana zina wata aba ce da shari'a da hankali suke ganin muninta, saboda ta keta alfarmar Ubangiji ce, da shiga haqqin macen, da haqqin danginta, da mijinta, kuma vatawa miji ne shimfixarsa, da cakuxa dangantaka da makamancin haka". (Tafsirin Assa'idiy).
       A wani wurin a cikin Alqur'ani mai tsarki Allah maxaukakin sarki ya siffata bayinsa muminai da cewa su ne waxanda ba sa zina, in da ya ce,"Waxanda ba sa kiran ko bautawa wani a tare da Allah, ba sa kashe ran da Allah ya haramta sai da haqqi, kuma ba sa zina, duk wanda ya aikata haka sai gamu da azaba" (Alfurqan : 78).
          Ya tabbata a cikin hadisi an tambayi Annabi (S.A.W) akan wane zunubi ne ya fi girma, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Shirka da Allah alhali shi ne ya halicce ka" sai aka ce sai wanne? Sai ya ce, "Sannan kashe xanka don kada ya ci tare da kai" sai aka ce "sannan sai wanne? Sai ya ce, "Ka yi zina da matar maqocinka" (Bukhari).
          Allah maxaukakin sarki ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma ya tava aure da jefe shi, namiji ko mace, idan kuwa bai tava aure ba, sai a yi masa bulala xari sannan a baquntar shi a wani gari daban tsawon shekara guda.
          Duk wanda ya kalli haddin zina zai ga yadda Allah ya kevance shi da wasu abubuwa saboda munin zina xin, daga cikin waxannan abubuwa akwai :
·        Kausasawa wajen uqubar mazinaci, ta hanyar jefewa. Ko kuma bulala da baquntarwa shekara guda.
Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya yayin da ake musu uquba. Allah ya ce"Mazinaciya da mazinaci ku yi kowane xaya daga cikinsu bulala xari, kada ku ji tausayinsu a cikin addinin Allah in dai kun yi imani da Allah da ranar qarshe".

  • Yi musu uquba a gaban mutane, ba a yarda a yi musu a voye ba, Allah ya ce 
Wasu vangare na muminai su halarci wajen yi musu uquba (haddi)" (Annur :2).
          Duk waxannan abubuwa suna nuna mana munin zina da rashin kyanta a musulunci. Imamul Bukhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa daga Maimun Al-audiy ya ce, "A lokacin jahiliyya na tava ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran birran suka taro suka jefe su".
          Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar maqocinsa. Allah ya kare mu.
Illolin Zina
        Babu ko shakka ga duk mai hankali cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, waxanda suke shafar mazinacin ko mazinaciyar, ko su shafi al'umma gaba xaya, ga wasu daga cikin illolinta :
1       Zubar da mutunci da jawo wa kai Kaskanci : domin duk matar da ta yi zina to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta kaskanci, ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya. Idan kuwa ta yi zina ta sami ciki sannan ta kashe dan, to ta hada laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai, in kuma ta bar shi to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tabewa, wanda hakan lalata duniya ce gaba daya.
2       Zina ta hada dukkan sharri gaba daya : saboda a cikin zina akwai, rashin tsoron Allah, da rashin kunya, da tsantseni, da rashin cika alqawari, da qarya, da butulci da sauransu.
3       Zina tana haifar da cututtuka, da mutuwar zuciya, da sanya ta bakikkirin, da samun kai cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa a ko yaushe. Bincike ya tabbatar da cewa cutar kanjamau ta fi yaduwa ta hanyar zina da fiye da kowace hanya da ake iya daukar cutar daga ita, sannan ta hanyar cuta akan kamu da muggan cututtuka masu mungun hadari.
4       Zina tana haifar da talauci da musiba a bayan kasa, saboda da duk namijin da yake mazinaci to ba ya iya tattali, kullum kudinsa suna wajen matan banza, kuma Allah ya kan zare masa albarka, don haka duk abin da zai samu ba zai amfanu da shi ba yadda ya dace, a banza zai tafi. Hakanan duk matar da take mazinaciya duk abin da ta samu yana qare wa ne wajen yadda zata janyo hankalin maza zuwa gare ta, kuma Allah zai zare wa dukiyarta albarka.
5       Zina tana kawo qiyayya da gaba tsakanin masu yin ta da sauran mutane, Allah madaukakin sarki yana cire musu kwarjini da girma daga idon mutane, saboda haka ne zaka ga qaramin yaro yana fada da sa'an kakansa a wurin neman mata, saboda ba ya qaunarsa ballantana ya girmama shi.
6       Zina tana jawo rashin amincewa da mai yin ta, kowa yana mai kallon maha'inci, mayaudari.
7       Zina tana haifar da wari daga cikin mai yinta, ba wanda yake jin wannan wari sai mutanen qwarai
8       Zina tana jawo azaba mai tsanani ga mai yin ta – idan bai tuba – a duniya da lahira. A duniya jefewa ko bulala da bakuntarwa, a lahira kuwa makomarsa wuta. Allah ya kare mu.
9       Zina tana kawo rugujewar gida da xaixacewar iyali, sannan tana kawo lalacewar tarbiyya.
10  A cikin zina akwai tozartar da dangantaka, da sanya cin dukiyar mutane ba da haqqi ba, domin kuwa duk xan da aka samu ta hanyar zina abin da zai gada ba haqqinsa ba ne.

Comments

Popular Posts