ILIMI GISHIRIN RAYUWAR DAN-ADAM

Da sunan Allah Mai Rahama Mai JinKai, Muna Gode Masa muna neman taimakonSa, Duk wanda Allah Ya shiriyar babu mai batar dashi, duk wanda Ya batar babu mai shiriyar dashi. Salati da Sallama ga Annabinmu, Abin koyinmu, Masoyinmu Muhammadu (S.A.W) da Ahalin Gidansa masu girma da Abokansa masu karamci. 
Ilimi shine Garkuwa kuma Gishirin rayuwar Dan-adam, shine yake kare dan-adam daga fadawa zuwa ga halaka da bata da lalacewa. Saboda girma da darajar ilimi, masanan yare basu bada wata cikakkiyar fassara ta ilimi ba, sai dai suka ce Ilimi shine Ilimi, wasu kuma suka ce Ilimi shine kishiyar Jahilci, wasu kuma suka ce Ilimi shine kasan abinda baka sani ba. To daga nan zamu iya gano darajar Ilimi, domin dole sai kayi amfani dashi wajen fito da fassarar sa. Saboda darajar Ilimi, maras shi ma, yana so a danganta shi da shi.Da zaka samu Jahili kace masa “Ya kai Jahili”tabbas sai kaga bacin ransa. Amma duk wanda kace masa “Mallam” (kana nufin Masani) to ko ba Masanin bane zai amsa, duk da cewa wasu suna cewa “Almajirin Mallam”.
A cikin abubuwan da Dan-adam yake fafutukar nema da tanadi, Ilimi ne kawai baya karewa. Kana iya shan wahala ka tara kudi kuma kudin su kare, kana iya fafutuka ka nemi Mulki, mulkin ya sulle maka, sannan kuma duk kana iya fita nemansu (Kudi da Mulkin) amma ka dawo gida baka samo su ba. Babu wanda ya taba fitowa daga gida zuwa neman Ilimi, ya koma gidan bai samo ba, haka kuma babu wanda ya taba samo Ilimi,Ilimin ya kare. Ya isa falalar Ilimi kasancewarsa abinda Allah (S.W.T) Ya daukaka Dan-adam saboda shi, Farkon halittar Annabi Adamu, Malaiku sunce “Ashe za Ka sanya a cikinta, wanda zai yi barna kuma ya zubar da jinane, alhali kuwa mu muna yi Maka tasbihi game da gode maka, kuma muna tsarkakewa gare Ka.” Ya ce “Lalle Ni Na san abin da baku sani ba” A wannan lokaci abin da Allah (SWT) Ya fara yi shine , baiwa Annabi Adamu Ilimi (Ya sanar dashi sunayen abubuwa), bayan Ya sanar da Shi, sai Ya tambayi Malaiku su fadi sunayen abubuwan, amma basu sani ba. Sai Ya umarci Annabi Adamu Ya sanar da su (Malaikun), da Ya sanar dasu sai Malaikun suka ce “Tsarki Ya tabbata a gareKa !! Babu sani a gare mu, face abinda Ka sanar damu, lallai ne Kai ne Masani Mai Hikima.”
Daga wannan zamu gano cewar lallai da Ilimi ne Dan-adam ya dara sauran halittun Allah daraja. Wani abin mamaki game da Ilimi shine, shi Ilimi ba'a jingina masa kalmar DA. Za'a iya cewa a DA wane Mai kudi ne, ko kuma a DA wane mai Mulki ne, amma ba ka taba ji ance a DA wane Mai-Ilimi bane. Ana iya zuwa ayi wa mutum Fashin Kudinsa, a wawashe shi tas, ko kuma ayi juyin Mulki ko zangon mulki ya kare, Mutum ya sauka daga kujerar Mulki. Amma ba za'a taba kwacewa Mutum abin da Ya sani ba. Ba'a taba jin cewar wasu 'yan-fashi sun kwace wa wani Malami Kararunsa ba, don haka bamu taba jin ance wane ai da Malami ne sosai, amma yanzu Jahili ne. Sai dai ana cewa wane Malami ne amma baya aiki da abinda ya Sani. Sannan kuma ita dukiya Mutum shi yake gadinta, amma Ilimi shi yake gadin Mutum, bayan haka kuma Ilimi shi yake raka mutum duk inda zai je, ba zaka taba jin Malami yazo guri ba an tambaye shi yace “Ai na baro karatun a gida” sai dai yace “Ban sani ba, amma zanje in bincika”.
Zan tsaya anan, amma Insha Allahu zan ci gaba

Comments

Popular Posts