Zan yi, zan yi, zan yi
Wannan shine babban abinda yafi ciwa mutanen wannan zamani tuwo a kwarya, Fasahar Sadarwa ta Zamani ta zo mana da abubuwan daukar hankali fiye da yadda muke tsammani. A kullum sai mu ce zamu yi amma bamu farawa saboda zurfin irin nitson da muke yi a duniyar yanar gizo. To ni dai insha Allahu zan dawo da rubutu a wannan Dandali nawa daga wani Satin idan Allah Ya amince min.