Zamani ! Zamani !! Zamani !!!

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai, godiya da yabo da kirari da jinjina su kara tabbata ga Shugaban Halittu, cikamakin Annabawa, shugaban Manzanni. Annabinmu, Masoyinmu, Abin koyinmu, Annabi Muhammadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da iyalan gidanSa da abokanSa da wanda suka bi hanyarSu har zuwa karshen al'amari.
Tabbas duk mai hankali da lura ya san muna cikin wani zamani mai cike da hayaniya da bankaura, zamanin da karya ta koma gaskiya, gaskiya ta koma karya, zamanin da mutunci ya koma kudi, kudi suka koma sune komai. Zamanin da iyaye suka koma 'ya'ya, Ya'ya suka koma iyaye, zamanin da baiwa ta koma Uwargiya, Uwargijiya ta koma baiwa, zamanin da baya ta koma gaba, gaba ta koma baya. Zamanin ci gaban mai ginin rijiya yana kara shiga kasa yana ganin yaci gaba, zamanin da ake girmama mara girma a kaskantar da mai girma. Zamanin da idan ka ce Allah sai a kalle ka a matsayin dan-kauye, Zamanin tafiya babu waiwaye, zamanin gudu babu jira, zamanin kowa ya tsira da kansa. Zamanin gaggawa, zamanin sauri ba wajen zuwa, zamanin bushewar zukata, zamanin kekashewar idaniya, zamanin yawan magana, zamanin karancin aiki, zamanin fada ba cikawa.
Ya Allah muna rokonKa da sunayenKa masu tsarki, don kadaitakar Zatinka Ya Allah, yadda ka sako mu ZAMANIN, Ya Allah Ka kare mu, Ka kare imaninmu.

Comments

Popular Posts