Begen Annabi
- Allahu Shi bani sani da basira, In yi yabo bakin karfina
- In yabi Sidi Muhammadu Bawa, Mai hana sauran bayi kuna
- Yi dadin tsira Allah da aminci, Gun Manzonka dare har rana
- Da alolinsa da kau kau sahabbansa, Masu sanin darajojin juna
- Da matayensa, da 'ya'yayeansa, Da mu mabiyansa darea har rana
Comments
Post a Comment